TAKE HA[EJANTATTUN KALMOMI DA ZANTUKA NA MUSAMMAN YAHAYA YUSUF ADM. NO: 1021106005 KUNDIN NEMAN DIGIRI NA FARKO, (BA HAUSA) WANDA AKA GABATAR A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU XANFODIYO, SAKKWATO. OKTOBA, 2014 i TABBATARWA Wannan aiki mai taken ‘Ha]ejantattun Kalmomi Da Zantuttuka Na Musamman’, an gudanar da shi a }ar}ashin kulawa da amincewar: …………………………… ………………………. Sa Hannun Mai Duba Aiki Kwanan Wata Mal. Sama’ila Umar …………………………… ………………………. Shugaban Sashen Kwanan Wata Prof. M. A. [antumbishi ………………………………….. ………………………. Sa Hannun Maidubawa Na Waje Kwanan Wata ii SADAUKARWA Na sadaukar da wannan aiki ga mahaifina marigayi Alhaji Yusuf [antamo da mahaifiyata Hajiya Hauwa’u Yusuf [antamo da ‘yan uwana baki ]aya da kuma matata Zainab Saleh Madaki da ]ana Muhammad Yahaya Yusuf (Saiyid). iii GODIYA Ina godiya da babbar murya ga Ubangijina makaxaici, Allah (SWT) da ya ba ni dama da ikon gudanar da wannan aikin a cikin sau}i da kwanciyar hankali, cikin ikonsa da }addarawarsa. Tsira da aminci su }ara tabbata ga Annabina Muhammad (SAW) da ahlihinsa da sahabbansa da duk masu biyar tafarkinsa har zuwa ranar }arshe. Har wa yau ina mi}a godiya wadda ba ta misaltuwa ga Mal. Sama’ila Umar, malamina wanda shi ya duba ni ya yi ha}uri da duk irin uzurin da na ba shi, na gode. Sannan ina godiya ga babban malaminmu baki ]aya wato Farfesa A. H. Amfani domin taimako da shawarwari da kayan aiki da kuma nuna kulawa da ya yi mana wajen gudanar da wannan aiki. Bazan manta da Mal. Idris Yahaya ba da kuma Mal. Sani Garba na Sashen Koyon Aikin Gona, wanda shi ne kamar tsanina a wannan jami’a. Ina sake mi}a godiya ga duk ]alibai abokaina da kuma uwa-uba matata da ta yi han}uri tun lokacin farkon aurenmu na taho tun tana kuka har ta saba. Allah ya yi mata sakamako mai kyau, amin. iv {UMSHIYA TAKE - - - - - - - - - i TABBATARWA - - - - - - - - ii SADAUKARWA - - - - - - - - iii GODIYA - - - - - - - - - iv {UMSHIYA - - - - - - - - v GABATARWA - - - - - - - - viii BABI NA [AYA 1.0 Shimfi]a - - - - - - - - 1 1.1 Bitar Ayyukan Da Suka Gabata - - - - 1 1.2 Dalilin Bincike - - - - - - - 5 1.3 MuhimmancinBincike - - - - - - 5 1.4 Hanyoyin Gudanar Da Bincike - - - - 6 1.5 Faxin Bincike - - - - - - - 7 1.6 Na]ewa - - - - - - - - 7 v BABI NA BIYU 2.0 Shimfi]a - - - - - - - - 8 2.1 Ma’anar Harshe - - - - - - - 8 2.2 Ma’anar Karin Harshe - - - - - - 9 2.3 Rabe-raben Karin Harshe n Hausa - - - - 10 2.4 Dalilan Da Suka Haifar Da Rabe-raben Karin Harshen Hausa - - - - - - - - 14 2.5 Naxewa - - - - - - - - 15 BABI NA UKU 3.0 Shimfi]a - - - - - - - - 16 3.1 Mene Ne Ha]ejanci? - - - - - - 17 3.2 Su Waye Ha]ejawa? - - - - - - 18 3.3 Ina Ne Ha]eja? - - - - - - - 19 3.4 Ha]ejantattun Kalmomi Da Suka Shafi Zance Na Yau Da Kullum - - - - - - - - 22 3.5 Ha]ejantattun Kalmomi Da Suka Shafi Sassan Jikin [an Adam - - - - - - - - 26 vi 3.6 Ha]ejantattun Kalmomi Da Suka Shafi Dabbobi Da Tsuntsaye - - - - - - - - 27 3.7 Ha]ejantattun Kalmomi Da Suka Shafi Abinci - - 28 3.8 Ha]ejantattun Kalmomi Da Suka Shafi Abubuwa Na Amfanin Yau Da Kullum - - - - - - - 30 3.9 Ha]ejantattun Kalmomi Da Suka Shafi Sarauta - - 32 3.10 Ha]ejantattun Kalmomi Da Suka Shafi Sunayen Mutane - 33 3.11 Na]ewa - - - - - - - - 34 BABI NA HU[U 4.0 Shimfi]a - - - - - - - - 36 4.1 Sassauqar Jimlar Hausa - - - - - - 37 4.2 Jimlar Korewa - - - - - - - 38 4.3 Jimlar Tambaya - - - - - - - 39 4.4 Jimlar Umarni - - - - - - - 40 4.5 Na]ewa - - - - - - - - 41 vii KAMMALAWA - - - - - - - - 43 MANAZARTA - - - - - - - - 45 RATAYE - - - - - - - - - 51 viii GABATARWA Wannan aiki mai taken ‘Ha]ejantattun Kalmomi Da Zantuka Na Musamman’, kamar yadda sunan ya nuna, aikin ya dogara ne kan kalmomi da zantuka waxanda suka ke~anta ga karin harshen Ha]ejanci. An kasa wannan aiki zuwa gida biyar. Kowane kashi babi ne mai zaman kansa. A babi na xaya gabatarwa ce ta aikin baki xaya, a cikin babin an kawo bitar ayyukan da suka gabata da dalilin bincike da muhimmancin bincike da hanyoyin gudanar da bincike da faxin bincike sannan naxewa. A babi na biyu, an gabatar da bayanai a kan ma’anar harshe da ma’anar karin harshe da rabe-raben karin harshe da kuma dalilan da suka haifar da karin harshe sannan naxewa. A babi na uku an kawo bayanai a kan mene ne Haxejanci da su waye Haxejawa da ina ne Haxeja da kuma Haxejantattun kalmomi da suka shafi zantukan yau da kullum da waxanda suka shafi sassan jikin xan Adam da waxanda suka shafi dabbobi da tsuntsaye da waxanda suka shafi abinci da waxanda suka shafi abubuwa na yau da kullum da waxanda suka shafi sarauta da kuma waxanda suka shafi sunayen mutane, sannan aka naxe babin. Babi na huxu ya kawo bayani a kan nau’o’in jimlolin Hausa kamar sassauqar jimlar Hausa da jimlar korewa da jimlar tambaya da kuma ix jimlar umarni, daga nan sai aka naxe babin. Sai kuma babi na biyar wanda a cikinsa aka kammala aikin gaba xayansa. A qarshe gaba xaya an kowa manazarta sannan rataye. x
Description: